A ranar Jummaa, 12 November 2020, an ba masu zaɓen Sarki guda huɗu takardan tambaya (query).
Wanda ake tamabaya sun haɗa Wazirin Zazzau, Makama Ƙarami, Limamin Jumma'a, da kuma Limamin Kona.
Takardan tambayan na tuhumar su akan rashin hallarta zama da aka gayyace su be ranar 30 October 2020.
A wannan lokacin ana shirye-shiryen ba da sandan Sarki, amma kotu ta hana su motsawa.
Ana buƙatar masu zaben Sarkin ne da su mai da martani cikin awa arba’in da takwas ko kuma gwamnati tayi musu hukunci.
Takardan query ta fito daga ofishin kwamishinan kanan hukumomi ne. Sakataren kananan hukumomi Musa Adamu ya sa hannu a man ko wane takardan.
Ana hasashen Gwamna El-Rufai da Sarkin Zazzau na so su cire masu zaɓen Sarkin ne don basu zaɓi sabon Sarki ba. Amma wannan ma zai ƙara matsala ne ba gyara ba, saboda sai an je kotu.
A halin yanzu dai ba mu ji daga mutanen gidan Fagacin Zazzau ba, saboda haka baza mu iya tantancewa ba ko an bashi takardan tambayan.
Daga cikin Fadar Zazzau
Comments