top of page
Writer's pictureBazazzage

Labari da ɗumi-ɗuminta

Updated: Oct 27, 2021

Rabon ƙasar Zazzau da ayi mata tsirara irin wannan tun zamanin Sarki Alu ɗan-Sidi wanda turawa suka cire saboda almundahana da cuwa-cuwa. Turawa ma sun kulle Madaki Saidu, a gidan yari, saboda mugun aiki da wasa dukiyan baitul mali. Madaki Saidu ɗan Sarki Alu ne. Tun lokacin, ba'a ƙara samun wani aikin bincike ba sai yanzu. Ku tabbata cewa kantoma ne ke haɗa fitina a ƙasar Zazzau, amma iyakansa watanni ƙalilan, in Allah ya yarda, kafin kotu tayi mana hukunci. Wannan labari mun yi kwananki muna tarawa. Mun tuntuɓi Barayan Sarki da Dando (wani yaron Turakin Zazzau da bai kai mu kawo sunansa anan ba) a ranan da Turaki yaje ya sadu da ɗan-Nasuru (muna nufin Kantoma, Amb. Bamalli). Mun ji daga wurin Dokajen Zazzau, munji daga wajen yaron Sarkin Fada a waya. Kuma mun karanta saƙon wani ɗan marigayi Sarki Shehu. Menene yasa Nasuru (Gwamna) binciken masaurata bisa shekara goma da suka wuce kawai? Kuma me yasa ba'ayi shekara biyar ko shekara ashirin ko arba'in? Burin wannan bincike zai cika in an cire mutane huɗu ne: a) Sarkin Kudu, b) Uban Gari, c) Dan Isa, d) Galadima. Kuma Limamin Jumma'a zai yi wuya ya sha. - daga majiya mai ƙarfi. Wannan bincike an fara ta ne daga shekara biyar da suka wuce, a lokacin d aka kira Ɗan Isa yazo yayi bayani akan wasu kuɗi kimanin miliyan ɗari huɗu (400 million) da suka kashe a shekara ta 2015. Ɗan Isa dai ya fasa ƙwai, ya faɗi wanda suka ci tare da shi. Tun daga nan abubuwa suka canza, ku karanta ku ji dalilai. 1. Wannan bincike dai ana yi ne don Nasuru (Gwamna) da ɗan-Nasuru (wato Kantoma) basu ji daɗin yadda yaran marigayi Sarki Shehu sukayi wandaƙa da kuɗin masarauta ba. Ku tuna Ɗan Isa da Ɗan Maje sun zama masu zagin kantoma akan Gwamna lokacin da marigayi na da rai. Sun san ƙananan mutane basu san halin girma ba. Abin ya fara damun Gwamna ne tun lokacin da aka kai mishi labarin yaran sun ƙona majalisar Sarki don su sami kwangilan gyarawa. Kuma sun samu. Abin bai yi ma ɗan-Nasuru daɗi ba. 2. In aka je fiye da shekara goma da suka wuce, akwai wasu yaran Sarki da zasu shiga maganan da ba'a so. Wa 'yannan yaran Fadan kuma su suke hura wutan ayi binciken. A yanzu ɗaya daga cikinsu shi ke rubuta ma ɗan-Nasuru takardan neman agaji zuwa ga gwamnonin Arewa. Ba mu ce a kira sunan Dokajen Zazzau ba, don ya zama zato kenan. (Muna ƙokarin samo takardan roƙo da aka rubuta ma Gwamnan Zamfara a yanzu haka.) 3. Wannan maganan bincike ta samu yarjejeniyar Turakin Zazzau ne. Baraya ɗan Jakadiya da Ciroman Shantaki sune shaidun mu, a ranan da Turaki ya sadu da ɗan-Nasuru a watan jiya. Shi Turaki yace ba hannunshi a kowace irin kwangila ta masaurata, Dokace ya tabbatar da wannan. Turaki dama ta kanshi yakeyi, har yanzu bashi da matsugunna. Ku fara mishi addu'a, abun kaman akwai hannu mutan ɓoye - inji Barayan Sarki. 4. Sarkin Fadan Zazzau dai shine ɗan gaban goshin ɗan-Nasuru ne. Kuma yana son kujerar Wazirin Zazzau. Har ma ɗan-Nasuru ya kai ma Nasuru maganar a Kaduna. A yanzu mutun ɗaya ke gabanshi - Galadiman Zazzau. A lokacin da Ɗan Isa yake ma masu bincike bayanin kashe kuɗi na shekara biyar da ya wuce, Ɗan Isa yace sun siya trelolin hatsi wurin Galadima sau da yawa. Kuma kowani trela ɗaya na hatsi sun biya sau uku ne. Kuma ba a lokacin suka fara ba. Wannan shiyasa aka ja binciken ya koma shekara goma memkon biyar. A cikin kuɗin da Ɗan Isa ake binciken almundahana, har an gina ma wani ɗan majalisa gida. Ɗan majalisan ya roƙe mu kar mu faɗa, saboda za'a iya daina bin shi sallan jummaa. 5. Cikin 'yan majalisa da ake zargi sun ci kuɗin, akwai masu raba ƙafa wurin Yariman Zazzau, da Iyan Zazzau don su samu agaji ko da ta ɓaci. Kaman Fagaci, da Sarkin Fulani, da Galadiman Zazzau. Galadima dai an shiga tsaka mai wuya, saboda basa zama a inuwa ɗaya da Waziri. Waziri baya zama da mai karkataccen zuciya. Mu dai fatan mu a kotu ta bamu Sarkin da Allah ya zaɓa mana. Sarki dogo, Sarki mai kama da mutane, kuma mai adalci. Allah ya raba mu da ɗan-Nasuru, na Annabi yace Amin. #Zazzau #Arewa #hausafulani #kaduna #hausa #bbchausa #voahausa #aminiya #biyora


Commentaires


bottom of page