Sarauta na nufin harka da ayyuka na tafiyar da harkokin jama’a na yau dakullum ga al’umma Hausa/Fulani. Wanda yake shugaba a wannan fannin shi ake kira Sarki. Akwai tsarin mulki na sarauta a kasar Hausa tun kafin zuwan Mujaddadi Shehu Usman Dan Fadiyo wanda da ya zo sai ya kara jaddada tsarin, ko da Turawa suka zo yankin kasar Hausa sun same su da tsarin sarautu wanda hakan ya sanya suka ci gaba da gudanar da tsarin tare da kawo wasu ‘yan sauye-sauye da ba su taka kara sun karya ba. Hasali ma sun dauki tsarin sun kai wasu yankuna a Nijeriya don gudanar da shi.
A kwanakin baya Allah ya yi wa Marigayi Dakta Shehu Idris, Sarkin Zazzau rasuwa bayan ya kwashe tsawon shekaru 45 yana kan karagar wannan sarauta. Allah ya jikansa da rahama ya sanya yana kyakkyawar matsayi. Tun daga mutuwar Mai Martaba hankula sun karkata kan wanda zai zama Sarki
Bisa tsarin sarautar Zazzau ana zaben sabon sarki ne daga gidajen masarautar guda hudu – wato daga Gidan Mallawa da Gidan Barebari da Gidan Katsinawa da kuma Gidan Sullubawa.
majalisar masu zaben sarkin Zazzau ta kunshi mutum biyar. Su za su zauna su tantance wadanda suka cancanta daga nan su tura wa gwamnan Jihar Kaduna sunayen mutum uku domin ya zabi daya a matsayin sabon sarki. Don haka sai abin da gwamna ya yanke.
Masu zaben sabon sarkin sun hada da Makaman Zazzau, Alhaji Muhammad Abbas da Fagacin Zazzau, Alhaji Umar Muhammad da Wazirin Zazzau, Alhaji Ibrahim Aminu da Limamin Kona Sheikh Muhammad Sani Aliyu da kuma Limamin Gari, Sheikh Dalhatu Kasim.
Cikin Ikon Allah wadannan mutane sun gudanar da zabensu a gaban sakataren gwamnatin Jihar Kaduna da Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Kaduna. Inda suka zabi Iyan Zazzau, Alhaji Bashar Aminu.
Ko da suka turawa gwamna sakamakon zaben sai ya nuna bai amince da zaben ba, a don haka ya bukaci a koma a sake wannan zaben. Amma daga baya ma sai ya nada wanda yake so.
A jawabinsa wajen nada sarki, El-Rufai ya yi da’awar cewa Ubangiji ya aiko shi domin ya gyara zaluncin da aka yi wa gidan Mallawa, domin Turawan mulkin mallaka sun yi rashin adalci wajen tunbuke Sarki Alu Dan-Sidi. Hujjoji sun tabbatar da cewa an an cire masa rawani ne saboda rashin gaskiya da cinikin bayi (duba litaffin M.G Smith, 1950). Za a iya jefa wannan zalunci a rukunin rashin gaskiya. Yin hakan yana nufin duka sarakunan da gwamnoni suka nada bayan shekarar 1920 ba na halal ba ne. Kenan, Amabasada Bamalli ne Sarkin gaskiya da aka nada a shekara 100.
Tun da yana ikirarin Ubangiji ya aiko shi ya yi gyara, sai ya fara la’akari da gidan Sullubawa da suka yi shekaru 160 babu mulki. Gidan Bare-bari da su ma sun yi shekaru 61 ba tare da mulki ba, amma ba su yi kukan rashin adalci ba.
A hannu daya kuma wasu wadanda wannan lamari bai shafe su ba, sun shigo ciki suna katsalandan don son zuciya da nuna cewa su wata tsiya ne bayan a lokacin da sarautar ta kucce masu a garuruwansu har shan ruwa a kasa aka yi don murna.
Sun zo suna ta fadin a yi hakuri kaddarar Allah ce, a yi hakuri ba sai an je kotu ba, sun manta sa da suke cewa za su je kotu a lokacin da suka rasa sarauta. Ai an yi kotu ne domin a fitar wa wanda aka zalunta hakkinsa.
Ko ma dai mene ne yanzu dai magana na kotu, wanda kuma a nan ne za a fitar wa wanda aka zalunta hakkinsa.Wannan abu yana nuna yadda ‘yan siyasa suka shiga ciki lamarin harkokin sarauta suka lalata saboda son zuciya da zalunci.
A karshe ina kira ga gwamnatin jihar Kaduna ta daina barazana ga masu zaben Sarki da suka nuna ra’ayinsu, wanda sun yi haka ne domin ci gaban al’ummarsu kasancewar shi Gwamnan da kansa ya hore su da cewa su yi Fi-sabilillahi, kuma sun yi hakan, amma don me za a nuna ba a yarda ba. Barazanar da ake yi masu shi ne a kan mukamansu da kuma rayuwarsu alal misali gwamnatin Jihar Kaduna ta dakatar da Wazirin Zazzau wanda shi ne shugaban kwamitin masu wannan zaben. Sai kuma wasoso da aka je kotun da ke sauraron wannan karar da aka yi. Wanda bayanai ma yana zuwa cewa ba a son a ci gaba da sauraron karar a wannan kotun.
Daga Dakta Nasir Aminu
Comments